1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An bude rumfunan zaben shugaban kasa a Chadi

May 6, 2024

An fara kada kuri'a a zaben shugaban kasar Chadi da hakan zai kawo karshen mulkin soji, da wasu ke kallo a matsayin sharar fage ga shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Mahamat Déby na ci gaba da rike madafun iko.

https://p.dw.com/p/4fX8x
Wata mai kada kuri'a a yankin Wahllokal da ke birnin N’djamena
Wata mai kada kuri'a a yankin Wahllokal da ke birnin N’djamenaHoto: Desire Danga Essigue/REUTERS

Mahamat Déby, ya hau kan mulkin kasar ta Chadi a 2021, bayan mutuwar mahaifinsa da ya mulki kasar tun daga 1990, zai fafata da tsohon Firaiministan kasar Success Masra, wanda ke kan gaba a adawa. Sauran 'yan takarar sun hada da tsohon Firaiministan kasar Albert Pahimi Padacke da wasu 'yan takarar guda bakwai.

Karin bayani: Fafutukar karshe ta yakin neman zabe a Chadi 

An kashe babban 'dan adawar da ake hasashen cewa zai kasancewa shugaban kadangaren-bakin tulu Yaya Diallo, a birnin N'Djamena, a ranar 28 ga watan Fabrairu wato ranar da aka sanar da lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasar a hukumance.

Karin bayani: Chadi: An hana wasu 'yan adawa takarar shugaban kasa

Shugaba Mahamat ya tabbatarwa da al'ummar kasar cewa gwamnatin wucin-gadi zai yi domin dora kasar kan gwadaben dimukradiyya anan gaba, duk da cewa 'yan adawa sun yi watsi kalaman shugaban.