1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

EU ta yi watsi da umurnin Isra'ila na kwashe mazauna Rafah

May 6, 2024

Babban jami'in diflomasiyyan Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce ba za a amince ba da umurnin ficewa da Isra'ila ta bai wa mazauna gabashin Rafah da ke a kudancin Gaza, birni daya tilo da ya ragewa al'ummar Falasdinu.

https://p.dw.com/p/4fYYH
Brüssel Josep Borrell bei Video-Konferenz
Hoto: Lenoir/EUC/Ropi/picture alliance

A cikin wani sako da ya wallafa a shifinsa na X, babban jami'in diflomasiyyan Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce wannan tsari zai iya kara dagula lamura tare da kara tsananin bala'in yunwar da ake fama da shi a zirin Gaza.

Kazalika babban jami'in diflomasiyyan ya kara da cewa ba zai yiwu a amince da wannan mataki ba, sannan kuma ya bukaci Isra'ila da ta jingine shirinta na kutsawa Rafah ta kasa tare da kiran kasashen duniya da kadda su bari a aikaita wannan kuskure.

Karin bayani: Isra'ila da Hamas sun gaza cimma matsaya kan yakin Gaza

A daya gefe kuma, gwamnatin Jamus ta yi kira ga bangarorin da ke gwabza fada a Gaza da kadda su kawo cikas ga tattaunawar da ake kan yiwiwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a daidai lokacin da wannan shiri ya fara samun turjiya daga masu tsatsauran ra'ayi na Isra'ila da Hamas. 

Kakakin fadar mulki ta Berlin ta ce ya zama wajibi bangarorin biyu su yayyafa wa zukatansu ruwan sanhi sannan su guji jefa makomar al'ummar yankin cikin hadari, domin ta hakane za a samu yanayin da zai ba da damar isar da kayan agaji da kuma sakin ragowar mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

Karin bayani: WFP: Gaza na cikin halin yunwa

Wannan gargadi na Jamus na zuwa ne a kwana guda bayan da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kawar da maganar tsagaita wuta na din-din-din da Hamas ta bukata, kazalika a daidai kuma lokacin da wani reshe na kungiyar Hamas din ya dauki alhakin cilla rokoki ga mashigar Kerem Shalom wanda ya kai Isra'ila ga daukar matakin katse shigar kayan agaji daga wannan mashigi.