1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Siyasar Jamus: Manhajar Tiktok na taka rawar gani ga matasa

May 6, 2024

Gabanin zaben 'yan majalisar EU a watan Yuni, manyan 'yan siyasar Jamus sun fara baza hajarsu ta kasuwar bukata a manhajar Tiktok, biyo bayan kuri'ar jin ra'ayin jama'a da ya nuna cewa matasan Jamus sun rungumi manhajar.

https://p.dw.com/p/4fX8z
Wani zanga-zangar matasan Jamus da ke sukar manufofin jam'iyyar AfD kan 'yan gudun hijra
Wani zanga-zangar matasan Jamus da ke sukar manufofin jam'iyyar AfD kan 'yan gudun hijraHoto: Sachelle Babbar/ ZUMAPRESS.com/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da ke yawan fuskantar barazana wajen amfani da shafukan sada zumunta ya dawo amfani da Tiktok gadan-gadan a watan Afrilun 2024, yayinda mataimakin shugaban gwamnatin Robert Habeck, ya rufa masa baya wajen amfani da manhajar duk da cewa a baya ya rufe shafukansa na facebook da Twitter domin dakile fuskantar fushin matasan zamani.

Karin bayani: Ranar Mata: 'Yancin zabe ga matan Jamus

Jam'iyyar AfD ce ke kan gaba wajen amfani da Tiktok da galibin matasa daga shekara 14 zuwa 29, da kuma kaso 22% na wadanda suka isa kada kuri'a ke rububin shiga jam'iyyar Alternative for Germany AfD.

Karin bayani: Jam'iyyun hadaka a Jamus sun gaza a zaben jihohin Bavaria da Hesse

Jamus na da kimanin mutune milyan 20 da ke amfani da Tiktok, a wani rahoton kididdiga da hukumomin kasar suka fitar, inda shekarun kaso 60% bisa 100 na masu amfani da manhajar, ya kama daga shekara 12 har zuwa 16 da kullum suke kan manhajar.